الحجر

Al-Hijr

Sura ta 15 · ta Makka · ayoyi 99 · Tsarin saukarwa: 54

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiA. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiRantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDaga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.