مريم
Maryam
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiK̃.H. Y.I. Ṣ̃.
- Abubakar Mahmoud GumiAmbaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!"
- Abubakar Mahmoud Gumi(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."
- Abubakar Mahmoud GumiYã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
- Abubakar Mahmoud GumiTa ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
- Abubakar Mahmoud GumiTa ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
- Abubakar Mahmoud GumiSai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
- Abubakar Mahmoud GumiSai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."
- Abubakar Mahmoud GumiWancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
- Abubakar Mahmoud GumiBã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ƙungiyõyin suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiMẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ambaci Ibrãhĩm a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina."
- Abubakar Mahmoud GumiTo, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya maɗaukaki.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma yã kasance yanã umurnin mutãnens da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
- Abubakar Mahmoud GumiMuka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.
- Abubakar Mahmoud GumiSai waɗansu 'yan bãya suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme.
- Abubakar Mahmoud GumiGidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiBã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice.
- Abubakar Mahmoud GumiWancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.
- Abubakar Mahmoud GumiShi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?"
- Abubakar Mahmoud GumiShin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?
- Abubakar Mahmoud GumiTo, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata. Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?"
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã.
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!"
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"
- Abubakar Mahmoud GumiShin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma suka riƙi gumãka, baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiA rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiBa su mal1akar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!"
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.
- Abubakar Mahmoud GumiSammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.
- Abubakar Mahmoud GumiAlhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.
- Abubakar Mahmoud GumiDukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?