الأنبياء

Al-Anbya

Sura ta 21 · ta Makka · ayoyi 112 · Tsarin saukarwa: 73

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiHisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani."
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko."
  1. Abubakar Mahmoud GumiWata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke, sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu a cikin wani sarari suKe iyo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAn halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiDã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su ba daga gareMu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa."
  1. Abubakar Mahmoud GumiMuka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka sanar da shi sana'ar wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa ga mãsu ibãda.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma mai kifi a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne wannan ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHar sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiDã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFirgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi."
  1. Abubakar Mahmoud GumiA rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta ga waɗansu mutãne mãsu ibãda.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa."