المؤمنون
Al-Mu'minun
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan, sũ ne magãda.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba.
- Abubakar Mahmoud GumiMuka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
- Abubakar Mahmoud GumiDa wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
- Abubakar Mahmoud GumiKuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiSai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani."
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiMashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."
- Abubakar Mahmoud GumiSai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.
- Abubakar Mahmoud GumiWata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni!
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne.
- Abubakar Mahmoud GumiZuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
- Abubakar Mahmoud GumiYã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.
- Abubakar Mahmoud GumiSai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
- Abubakar Mahmoud GumiMunã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su.
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiHar idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya.
- Abubakar Mahmoud GumiKunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha.
- Abubakar Mahmoud GumiShin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu?
- Abubakar Mahmoud GumiKõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi?
- Abubakar Mahmoud GumiKõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.
- Abubakar Mahmoud GumiHar idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa.
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lal1e ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko."
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?"
- Abubakar Mahmoud GumiZã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?"
- Abubakar Mahmoud GumiZã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?"
- Abubakar Mahmoud GumiZã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?"
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
- Abubakar Mahmoud GumiAllah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiMasanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiKa tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, "
- Abubakar Mahmoud GumiHar idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama.
- Abubakar Mahmoud GumiFuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi."
- Abubakar Mahmoud GumiSai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiAllah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama."