لقمان

Luqman

Sura ta 31 · ta Makka · ayoyi 34 · Tsarin saukarwa: 57

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiA. L̃. M̃.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda ke tsai da salla kuma sunã ɓãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, "Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma idan mahaifanka suka tsananta maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kada ka karkatar da kundukukinka ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna. "
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu? Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa." shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa ga azãbar sa'ir,
  1. Abubakar Mahmoud Gumikuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to, lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMunã jĩshe su dãdi kaɗan sa'an nan Mu tĩlasta su ga shiga zuwa azãba kakkaura.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?" Lalle zã su ce: "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah" Ã'a, mafi yawansu ba su sani ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAbin da yake a cikin sammai da ƙasa duka na Allah kawai ne. Lalle, Allah Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba. Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHalittarku bã ta zama ba, kuma tãyar da ku bai zama ba, fãce kamar rai guda. Lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan fa dõmin Allah Shĩ ne Gaskiya, kuma abin da suke kira wanda bã Shi ba, shi ne ƙaryã, kuma lalle, A1lah shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, mai gõdiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu, sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce dukkan mayaudari mai yawan kãfirci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini, rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin nan ya rũɗẽ ku game da Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa.