الفرقان
Al-Furqan
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiAlbarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.
- Abubakar Mahmoud Gumiwanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma."
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi?
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce:"
- Abubakar Mahmoud GumiKa dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki.
- Abubakar Mahmoud GumiAlbarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje.
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a.
- Abubakar Mahmoud GumiIdan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can.
- Abubakar Mahmoud GumiKada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa.
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"
- Abubakar Mahmoud Gumisuka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku."
- Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiA rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe mu!"
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya.
- Abubakar Mahmoud GumiMa'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa.
- Abubakar Mahmoud GumiMulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo!
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba!
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa!"
- Abubakar Mahmoud GumiKuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yinMu." sai Muka darkãke su, darkãkewa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai.
- Abubakar Mahmoud GumiDa Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo?
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!
- Abubakar Mahmoud GumiShin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa?
- Abubakar Mahmoud GumiKo kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama.
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi a ciƙin kõwace alƙarya.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiBa Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi.
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya zuwa ga Ubangijinsa."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi.
- Abubakar Mahmoud GumiIdan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙãra musu gudu.
- Abubakar Mahmoud GumiAlbarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bãyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,
- Abubakar Mahmoud GumiA riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce.
- Abubakar Mahmoud GumiSai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya tũba, kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame da makãfi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga mãsu taƙawa."
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci.
- Abubakar Mahmoud GumiSuna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni.
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci."