الشعراء
Ash-Shu'ara
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud Gumi¦. S̃. M̃.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
- Abubakar Mahmoud GumiTsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
- Abubakar Mahmoud GumiIdan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
- Abubakar Mahmoud GumiFir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!
- Abubakar Mahmoud Gumi"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."
- Abubakar Mahmoud GumiSai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?
- Abubakar Mahmoud Gumi"Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."
- Abubakar Mahmoud GumiTo, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."
- Abubakar Mahmoud GumiMũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."
- Abubakar Mahmoud GumiSai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
- Abubakar Mahmoud GumiSai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ubangijin Mũsa da Hãrũna."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
- Abubakar Mahmoud GumiDa taskõki da mazauni mai kyau.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
- Abubakar Mahmoud GumiA sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."
- Abubakar Mahmoud Gumi"A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"
- Abubakar Mahmoud GumiSai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun.
- Abubakar Mahmoud GumiDa rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
- Abubakar Mahmoud Gumi"Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."
- Abubakar Mahmoud Gumi"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã mu da abõki, masõyi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiMutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."
- Abubakar Mahmoud Gumi"To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ban zama mai kõre mũminai ba."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."
- Abubakar Mahmoud GumiSai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
- Abubakar Mahmoud GumiÃdãwa sun ƙaryata Manzanni.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."
- Abubakar Mahmoud Gumi"To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Da gõnaki da marẽmari."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen mutãnen farko."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiSamũdãwa sun ƙaryata Manzanni.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, anã barin ku a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"A cikin gõnaki da marẽmari."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan yini, kuma kunã da shan yini sasanne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiMutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma Muka darkãke wasu.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiMa'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."
- Abubakar Mahmoud Gumi"To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.
- Abubakar Mahmoud GumiRũhi amintacce ne ya sauka da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiA kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.
- Abubakar Mahmoud GumiDa harshe na Larabci mai bayãni.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,
- Abubakar Mahmoud GumiYa karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
- Abubakar Mahmoud GumiBã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.
- Abubakar Mahmoud GumiSai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, to, da azãbarMu suke nẽman gaggãwa?
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,
- Abubakar Mahmoud GumiAbin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare su.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka sassauta fikãfikanka ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.
- Abubakar Mahmoud GumiDa jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle Shi, Shi ne Mai ji, Masani.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, (kunã so) in gaya muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?
- Abubakar Mahmoud GumiSukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mawãƙa halakakku ne ke bin su.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?
- Abubakar Mahmoud GumiFãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.