الصافات

As-Saffat

Sura ta 37 · ta Makka · ayoyi 182 · Tsarin saukarwa: 56

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiUbangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiIdan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKu tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMe ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan sunã da abinci sananne.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAnã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFarã mai dãɗi ga mashãyan.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMuka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Me ya sãme ku, bã ku magana?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAminci ya tabbata ga Ilyãs.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, bã ku tunãni?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
  1. Abubakar Mahmoud GumiTsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
  1. Abubakar Mahmoud GumiBa ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.