ص

Sad

Sura ta 38 · ta Makka · ayoyi 88 · Tsarin saukarwa: 38

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiṢ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu).
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiShũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu).
  1. Abubakar Mahmoud GumiRundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa).
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, waɗancan ne ƙungiyõyin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima da rarrabẽwar magana.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurinMu, da kyaun makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, a lõkacin maraice.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna. Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Muka hõre masa iska tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiJahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wani daga siffarsa nau'i-nau'i.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma".
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Zuwa ga yinin lõkaci sananne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce, "To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa a bayan ɗan lõkaci."