الزخرف

Az-Zukhruf

Sura ta 43 · ta Makka · ayoyi 89 · Tsarin saukarwa: 63

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiḤ. M̃.
  1. Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kuwa sau nawa Muka aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko!
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su."
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDomin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka sanya Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe?
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Fãce wannan da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun nan biyu ba?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHar a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, kõ dai Mu tafi da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ƙungiyõyi suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi!
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMasõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne).
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKu shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAnã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane (da haka).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani.