الدخان
Ad-Dukhan
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiḤ. M̃.
- Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
- Abubakar Mahmoud GumiUmurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
- Abubakar Mahmoud GumiBabu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
- Abubakar Mahmoud GumiA'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
- Abubakar Mahmoud GumiYanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
- Abubakar Mahmoud GumiYa Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
- Abubakar Mahmoud GumiInã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."
- Abubakar Mahmoud GumiSai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."
- Abubakar Mahmoud GumiDa yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
- Abubakar Mahmoud GumiDa shuke-shuke da matsayi mai kyau.
- Abubakar Mahmoud GumiDa wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiDaga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna
- Abubakar Mahmoud GumiLalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,
- Abubakar Mahmoud Gumi"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
- Abubakar Mahmoud Gumishin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
- Abubakar Mahmoud GumiBa Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
- Abubakar Mahmoud Gumifãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),
- Abubakar Mahmoud GumiIta ce abincin mai laifi.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar tafasar ruwan zãfi.
- Abubakar Mahmoud Gumi(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).
- Abubakar Mahmoud GumiBã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.