ق
Qaf
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud Gumi¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
- Abubakar Mahmoud GumiDa ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiDa itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
- Abubakar Mahmoud GumiMutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiDa Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
- Abubakar Mahmoud GumiDa ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
- Abubakar Mahmoud GumiBã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
- Abubakar Mahmoud GumiKuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
- Abubakar Mahmoud GumiAbõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
- Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa."
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?"
- Abubakar Mahmoud GumiKuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
- Abubakar Mahmoud Gumi"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama."
- Abubakar Mahmoud GumiSunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu).
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
- Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
- Abubakar Mahmoud GumiMũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.