الذاريات

Adh-Dhariyat

Sura ta 51 · ta Makka · ayoyi 60 · Tsarin saukarwa: 67

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).
  1. Abubakar Mahmoud GumiAnã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
  1. Abubakar Mahmoud GumiAn la'ani mãsu ƙiri-faɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiRanar da suke a kan wuta anã fitinar su.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBa su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
  1. Abubakar Mahmoud Gumishin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.