الواقعة

Al-Waqi'ah

Sura ta 56 · ta Makka · ayoyi 96 · Tsarin saukarwa: 46

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiIdan mai aukuwa ta auku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiIdan aka girgiza ƙasã girgizwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kun kasance nau'i uku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWatau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA ckin Aljannar ni'ima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiJama'a ne daga mutãnen farko.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wani ruwa mai gudãna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su yankẽwa kuma bã a hana su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wasu shimfiɗu maɗaukaka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Muka sanya su budurwai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGa mazõwa dãma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
  1. Abubakar Mahmoud GumiA kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikin wani littafi tsararre.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKu mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa ƙõnuwa da Jahĩm,
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.