الرحمن

Ar-Rahman

Sura ta 55 · ta Madina · ayoyi 78 · Tsarin saukarwa: 97

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Allah) Mai rahama.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã sanar da Alƙur'ani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã halitta mutum.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã sanar da shi bayãni (magana).
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnã da watã a kan lissãfi suke.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiUbangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud Gumiwanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiZã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAnã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud Gumizã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiWannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu rassan itãce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu duhun inuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiWani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.