القلم

Al-Qalam

Sura ta 68 · ta Makka · ayoyi 52 · Tsarin saukarwa: 2

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiÑ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDon haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGa wanenku haukã take.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSaboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai zunɗe, mai yãwo da gulma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiIdan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiZã Mu yi masa alãma a kan hanci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiCẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiMafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiHaka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMe ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiCẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRanar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSu fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiIna jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBa dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiShi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.