الحاقة

Al-Haqqah

Sura ta 69 · ta Makka · ayoyi 52 · Tsarin saukarwa: 78

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiKiran gaskiya!
  1. Abubakar Mahmoud GumiMẽne ne kiran gaskiya?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSamũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikin Aljanna maɗaukakiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiNunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ĩkona ya ɓace mini!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa abin da bã ku iya gani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAbin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDã Mun kãma shi da dãma.
  1. Abubakar Mahmoud Gumisa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.