نوح

Nuh

Sura ta 71 · ta Makka · ayoyi 28 · Tsarin saukarwa: 71

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
  1. Abubakar Mahmoud GumiNũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
  1. Abubakar Mahmoud GumiNũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka."