المعارج
Al-Ma'arij
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiWani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiGa kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiDaga Allah Mai matãkala.
- Abubakar Mahmoud GumiMalã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
- Abubakar Mahmoud GumiAna sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
- Abubakar Mahmoud GumiDa matarsa da ɗan'uwansa.
- Abubakar Mahmoud GumiDa danginsa, mãsu tattarã shi.
- Abubakar Mahmoud GumiDa wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
- Abubakar Mahmoud GumiMai twãle fãtar goshi.
- Abubakar Mahmoud GumiTanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
- Abubakar Mahmoud GumiYa tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
- Abubakar Mahmoud GumiIdan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSai mãsu yin salla,
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
- Abubakar Mahmoud GumiGa (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
- Abubakar Mahmoud GumiMẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
- Abubakar Mahmoud GumiDaga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
- Abubakar Mahmoud GumiShin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiGa Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiMaƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)