المدثر
Al-Muddaththir
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiYã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
- Abubakar Mahmoud GumiKa tãshi dõmin ka yi gargaɗi
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
- Abubakar Mahmoud GumiKada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
- Abubakar Mahmoud GumiKuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
- Abubakar Mahmoud GumiTo, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
- Abubakar Mahmoud GumiA kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKa bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
- Abubakar Mahmoud GumiDa ɗiyã halartattu,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
- Abubakar Mahmoud GumiFaufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.
- Abubakar Mahmoud GumiZã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, ya yi tunãni
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,
- Abubakar Mahmoud GumiSai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Wannan maganar mutum dai ce."
- Abubakar Mahmoud GumiZã Ni ƙõna shi da Saƙar.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!
- Abubakar Mahmoud GumiBã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.
- Abubakar Mahmoud GumiMai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).
- Abubakar Mahmoud GumiA kanta akwai (matsara) gõma shã tara.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Ina rantsuwa da watã.
- Abubakar Mahmoud GumiDa dare a lõkacin da ya jũyar da baya.
- Abubakar Mahmoud GumiDa sãfiya idan ta wãye.
- Abubakar Mahmoud GumiIta (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.
- Abubakar Mahmoud GumiMai gargaɗĩ ce ga mutum.
- Abubakar Mahmoud GumiGa wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.
- Abubakar Mahmoud GumiKõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce mutãnen dãma.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikin Aljanna suna tambayar jũna.
- Abubakar Mahmoud GumiGame da mãsu laifi.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
- Abubakar Mahmoud GumiHaba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSun gudu daga zãki.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin wanda ya so, ya tuna.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.