القيامة

Al-Qiyamah

Sura ta 75 · ta Makka · ayoyi 40 · Tsarin saukarwa: 31

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiNa'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBa haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
  1. Abubakar Mahmoud GumiAka tãra rãnã da watã
  1. Abubakar Mahmoud GumiMutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! bãbu mafaka.
  1. Abubakar Mahmoud Gumizuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAna gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBa haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
  1. Abubakar Mahmoud Gumisa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
  1. Abubakar Mahmoud GumiWasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiZuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
  1. Abubakar Mahmoud Gumikuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiZuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
  1. Abubakar Mahmoud GumiAmma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHalaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiBai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?