الزلزلة
Az-Zalzalah
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiIdan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
- Abubakar Mahmoud GumiA rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
- Abubakar Mahmoud Gumicewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
- Abubakar Mahmoud GumiA rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.