العاديات
Al-'Adiyat
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
- Abubakar Mahmoud GumiMãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
- Abubakar Mahmoud GumiSai su motsar da ƙũra game da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiSai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
- Abubakar Mahmoud GumiAka bayyana abin da ke cikin zukata.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?