القارعة
Al-Qari'ah
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiMai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
- Abubakar Mahmoud GumiMẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
- Abubakar Mahmoud GumiTo, uwarsa Hãwiya ce.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma me ya sanar da kai mece ce ita?
- Abubakar Mahmoud GumiWata wuta ce mai zafi.