التكاثر

At-Takathur

Sura ta 102 · ta Makka · ayoyi 8 · Tsarin saukarwa: 16

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
  1. Abubakar Mahmoud GumiHar kuka ziyarci kaburbura.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, tabbas, zã ku sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHaƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne da kuna ganin Jahĩm.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).