العصر

Al-'Asr

Sura ta 103 · ta Makka · ayoyi 3 · Tsarin saukarwa: 13

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da zãmani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne mutum yana a cikin hasara.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).