الهمزة
Al-Humazah
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
- Abubakar Mahmoud GumiWanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiYana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
- Abubakar Mahmoud GumiWutar Allah ce wadda ake hurawa.
- Abubakar Mahmoud GumiWadda take lẽƙãwa a kan zukata.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.