الفيل
Al-Fil
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
- Abubakar Mahmoud GumiSuna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?