الطور
At-Tur
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).
- Abubakar Mahmoud GumiDa wani littãfi rubũtacce.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
- Abubakar Mahmoud GumiDa Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).
- Abubakar Mahmoud GumiDa rufin nan da aka ɗaukaka.
- Abubakar Mahmoud GumiDa tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
- Abubakar Mahmoud GumiLalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
- Abubakar Mahmoud GumiBã ta da mai tunkuɗẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
- Abubakar Mahmoud Gumi"To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"
- Abubakar Mahmoud Gumi"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.
- Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."
- Abubakar Mahmoud Gumi"To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama."
- Abubakar Mahmoud GumiTo, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.
- Abubakar Mahmoud GumiShin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?
- Abubakar Mahmoud GumiKa ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."
- Abubakar Mahmoud GumiShin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiRãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri.