النجم
An-Najm
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
- Abubakar Mahmoud GumiMa'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
- Abubakar Mahmoud GumiMa'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
- Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
- Abubakar Mahmoud GumiHar ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).
- Abubakar Mahmoud GumiZũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.
- Abubakar Mahmoud GumiA wurin da magaryar tuƙẽwa take.
- Abubakar Mahmoud GumiA inda taken, nan Aljannar makoma take.
- Abubakar Mahmoud GumiLõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
- Abubakar Mahmoud GumiGaninsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, kun ga Lãta da uzza?
- Abubakar Mahmoud GumiDa (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
- Abubakar Mahmoud GumiWannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
- Abubakar Mahmoud GumiKo (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
- Abubakar Mahmoud GumiTo, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
- Abubakar Mahmoud GumiAkwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
- Abubakar Mahmoud GumiWannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, ka ga wannan da ya jũya baya?
- Abubakar Mahmoud GumiYa yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?
- Abubakar Mahmoud GumiShin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
- Abubakar Mahmoud GumiKo kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
- Abubakar Mahmoud GumiDa Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?
- Abubakar Mahmoud GumiCẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
- Abubakar Mahmoud GumiDaga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
- Abubakar Mahmoud GumiDa Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
- Abubakar Mahmoud GumiDa mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
- Abubakar Mahmoud GumiDa waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
- Abubakar Mahmoud Gumiwannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
- Abubakar Mahmoud GumiMakusanciya fa, tã yi kusa.
- Abubakar Mahmoud GumiBãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
- Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kunã mãsu wãsã?
- Abubakar Mahmoud GumiTo, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).