القمر

Al-Qamar

Sura ta 54 · ta Makka · ayoyi 55 · Tsarin saukarwa: 37

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiSã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiMutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSamũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiZã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiZã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.