الانسان
Al-Insan
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.
- Abubakar Mahmoud GumiWani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSuna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.
- Abubakar Mahmoud Gumi"Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa."
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
- Abubakar Mahmoud Gumi¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
- Abubakar Mahmoud GumiAna shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
- Abubakar Mahmoud GumiWani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba.
- Abubakar Mahmoud GumiTufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki).
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
- Abubakar Mahmoud GumiDaga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
- Abubakar Mahmoud GumiMũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.
- Abubakar Mahmoud GumiYana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.