المرسلات
Al-Mursalat
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
- Abubakar Mahmoud Gumisa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
- Abubakar Mahmoud GumiDomin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
- Abubakar Mahmoud GumiTo, idan taurãri aka shãfe haskensu.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, idan sama aka tsãge ta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, idan duwãtsu aka nike su.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
- Abubakar Mahmoud GumiDomin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
- Abubakar Mahmoud GumiDomin rãnar rarrabẽwa.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
- Abubakar Mahmoud GumiBone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
- Abubakar Mahmoud GumiHaka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
- Abubakar Mahmoud GumiBone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
- Abubakar Mahmoud GumiZuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
- Abubakar Mahmoud GumiGa rãyayyu da matattu,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiKu tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
- Abubakar Mahmoud GumiKu tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
- Abubakar Mahmoud GumiIta ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
- Abubakar Mahmoud GumiKamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiWannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
- Abubakar Mahmoud GumiBã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiWannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
- Abubakar Mahmoud GumiDa wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
- Abubakar Mahmoud Gumi(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud Gumi(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
- Abubakar Mahmoud GumiTo, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni