النبإ

An-Naba

Sura ta 78 · ta Makka · ayoyi 40 · Tsarin saukarwa: 80

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiA kan mẽ suke tambayar jũna?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Zã su sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, a'aha! Zã su sani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa itãcen lambuna mãsu lillibniya?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGa mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSakamako mai dãcẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLambuna da inabõbi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa hinjãlan giya cikakku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiUbangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"