النازعات

An-Nazi'at

Sura ta 79 · ta Makka · ayoyi 46 · Tsarin saukarwa: 81

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSuka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai kawai gã su a bãyan ƙasa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYa fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa duwatsu, Yã kafe ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDomin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, amma wanda ya yi girman kai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?
  1. Abubakar Mahmoud GumiMe ya haɗã ka da ambatonta?
  1. Abubakar Mahmoud GumiZuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.