عبس

'Abasa

Sura ta 80 · ta Makka · ayoyi 42 · Tsarin saukarwa: 24

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã game huska kuma ya jũya bãya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda makãho yã je masa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAmma wanda ya wadãtu da dũkiya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKai kuma kã shagala ga barinsa!
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
  1. Abubakar Mahmoud Gumi(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
  1. Abubakar Mahmoud GumiAbãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikin hannãyen mala'iku marubũta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAn la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
  1. Abubakar Mahmoud GumiDaga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDaga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiHaƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa inabi da ciyãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa zaitũni da itãcen dabĩno.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa lambuna, mãsu yawan itãce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDomin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa uwarsa da ubansa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mãtarsa da ɗiyansa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGa kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBaƙi zai rufe su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).