التكوير

At-Takwir

Sura ta 81 · ta Makka · ayoyi 29 · Tsarin saukarwa: 7

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiIdan rãna aka shafe haskenta
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
  1. Abubakar Mahmoud Gumi"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
  1. Abubakar Mahmoud GumiIdan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sama aka fẽɗe ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan Jahĩm aka hũra ta
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMãsu gudu suna ɓũya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa dare idan ya bãyar da bãya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa sãfiya idan ta yi lumfashi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, a inã zã ku tafi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGa wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.