الإنفطار
Al-Infitar
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiIdan sama ta tsãge.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan taurãri suka wãtse.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan tẽkuna aka facce su.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan kaburbura aka tõne su.
- Abubakar Mahmoud GumiRai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
- Abubakar Mahmoud GumiYã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
- Abubakar Mahmoud GumiMãsu daraja, marubũta.
- Abubakar Mahmoud GumiSunã sanin abin da kuke aikatãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
- Abubakar Mahmoud GumiZã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
- Abubakar Mahmoud GumiBã zã su faku daga gare ta ba.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
- Abubakar Mahmoud GumiRãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.