المطففين
Al-Mutaffifin
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiBone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
- Abubakar Mahmoud GumiAshe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
- Abubakar Mahmoud GumiDomin yini mai girma.
- Abubakar Mahmoud GumiYinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
- Abubakar Mahmoud GumiHaƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
- Abubakar Mahmoud GumiWani 1ittãfi ne rubũtacce.
- Abubakar Mahmoud GumiBone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
- Abubakar Mahmoud GumiBabũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
- Abubakar Mahmoud GumiIdan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
- Abubakar Mahmoud GumiWani littãfi ne rubũtacce.
- Abubakar Mahmoud GumiMuƙarrabai suke halarta shi.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
- Abubakar Mahmoud GumiA kan karagu, suna ta kallo.
- Abubakar Mahmoud GumiKana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
- Abubakar Mahmoud GumiAna shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
- Abubakar Mahmoud Gumi¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
- Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
- Abubakar Mahmoud GumiA kan karagu, suna ta kallo.
- Abubakar Mahmoud GumiShin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?