الإنشقاق
Al-Inshiqaq
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiIdan sama ta kẽce,
- Abubakar Mahmoud GumiTa saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
- Abubakar Mahmoud GumiYa kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, zã shi dinga kiran halaka!
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ya shiga sa'ĩr.
- Abubakar Mahmoud GumiLal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
- Abubakar Mahmoud GumiNa'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
- Abubakar Mahmoud GumiDa dare, da abin da ya ƙunsa.
- Abubakar Mahmoud GumiDa watã idan (haskensa) ya cika.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
- Abubakar Mahmoud GumiBa haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
- Abubakar Mahmoud GumiAlhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
- Abubakar Mahmoud GumiSaboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.