البروج

Al-Buruj

Sura ta 85 · ta Makka · ayoyi 22 · Tsarin saukarwa: 27

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
  1. Abubakar Mahmoud GumiAn la'ani mutãnen rãmi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWato wuta wadda aka hura.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai Al'arshi mai girma
  1. Abubakar Mahmoud GumiMai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo lãbãrin rundanõni yã zo maka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFir'auna da samũdãwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
  1. Abubakar Mahmoud GumiÃ'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA cikin Allo tsararre.