الطارق

At-Tariq

Sura ta 86 · ta Makka · ayoyi 17 · Tsarin saukarwa: 36

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShi ne taurãron nan mai tsananin haske.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAn halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiRãnar da ake jarrabawar asirai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSaboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
  1. Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma shĩ bã bananci bane
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSaboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.