الأعلى
Al-A'la
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiKa tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
- Abubakar Mahmoud GumiZa mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
- Abubakar Mahmoud GumiWanda zai shiga wutar da tã fi girma.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
- Abubakar Mahmoud GumiBa haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
- Abubakar Mahmoud GumiAlhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
- Abubakar Mahmoud GumiLittaffan Ibrãhĩm da Mũsã.