الغاشية
Al-Ghashiyah
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
- Abubakar Mahmoud GumiWasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
- Abubakar Mahmoud GumiMãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
- Abubakar Mahmoud GumiZã su shiga wata wuta mai zãfi.
- Abubakar Mahmoud GumiAna shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
- Abubakar Mahmoud GumiBa su da wani abinci fãce dai daga danyi.
- Abubakar Mahmoud GumiBã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
- Abubakar Mahmoud GumiWasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
- Abubakar Mahmoud GumiGame da aikinsu, masu yarda ne.
- Abubakar Mahmoud Gumi(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
- Abubakar Mahmoud GumiBã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikinta akwai marmaro mai gudãna.
- Abubakar Mahmoud GumiA cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
- Abubakar Mahmoud GumiDa kõfuna ar'aje.
- Abubakar Mahmoud GumiDa filõli jẽre,
- Abubakar Mahmoud GumiDa katifu shimfiɗe.
- Abubakar Mahmoud GumiAshe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
- Abubakar Mahmoud GumiDa zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
- Abubakar Mahmoud GumiDa zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
- Abubakar Mahmoud GumiDa zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
- Abubakar Mahmoud Gumisabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
- Abubakar Mahmoud GumiBa ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
- Abubakar Mahmoud GumiFãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
- Abubakar Mahmoud GumiTo, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.