الفجر

Al-Fajr

Sura ta 89 · ta Makka · ayoyi 30 · Tsarin saukarwa: 10

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da alfijiri.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa darũruwa gõma.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa (adadi na) cikã da (na) mãrã.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa dare idan yana shũɗewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiBa ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiIramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa Fir'auna mai turãku.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
  1. Abubakar Mahmoud GumiYana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiYã kai rai mai natsuwa!
  1. Abubakar Mahmoud GumiKa koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).