البلد

Al-Balad

Sura ta 90 · ta Makka · ayoyi 20 · Tsarin saukarwa: 35

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiBã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa mahaifi da abin da ya haifa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
  1. Abubakar Mahmoud GumiYana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa,"
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiShin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa harshe, da leɓɓa biyu.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
  1. Abubakar Mahmoud GumiIta ce fansar wuyan bãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiGa marãya ma'abũcin zumunta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKo kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWaɗannan ne ma'abũta albarka
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci
  1. Abubakar Mahmoud GumiA kansu akwai wata wuta abar kullewa.