الشمس
Ash-Shams
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiIna rantsuwa da rãnã da hantsinta.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma da wata idan ya bi ta.
- Abubakar Mahmoud GumiDa yini a lõkacin da ya bayyana ta.
- Abubakar Mahmoud GumiDa dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
- Abubakar Mahmoud GumiDa sama da abin da ya gina ta.
- Abubakar Mahmoud GumiDa ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
- Abubakar Mahmoud GumiDa rai da abin da ya daidaita shi.
- Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.
- Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.
- Abubakar Mahmoud GumiSamũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
- Abubakar Mahmoud GumiA lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
- Abubakar Mahmoud GumiSai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
- Abubakar Mahmoud GumiSai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).