الليل

Al-Layl

Sura ta 92 · ta Makka · ayoyi 21 · Tsarin saukarwa: 9

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa abin da ya halitta namiji da mace.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
  1. Abubakar Mahmoud GumiLãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiBãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma mafi taƙawa zai nisance ta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiWanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAlhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
  1. Abubakar Mahmoud GumiFãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).