الضحى

Ad-Duhaa

Sura ta 93 · ta Makka · ayoyi 11 · Tsarin saukarwa: 11

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da hantsi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
  1. Abubakar Mahmoud GumiUbangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
  1. Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiKuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).