الشرح
Ash-Sharh
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiBa Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda ya nauyayi bãyanka?
- Abubakar Mahmoud GumiKuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
- Abubakar Mahmoud GumiTo, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
- Abubakar Mahmoud GumiSabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
- Abubakar Mahmoud GumiKuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.